Abdi hassan Muhammed
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Abdi Hassan Muhammed "Hijaar" ( Somali , Larabci: عبدي حسن محمد حجار ) babban jami'in 'yan sandan Somaliya ne kuma tsohon jami'in Soja. Shi ne kwamishinan 'yan sanda na rundunar 'yan sandan Somaliya a halin yanzu .
Farkon rayuwa da karatu
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Hijar a yankin Sool a shekarar 1953. Ya kammala karatunsa na firamare a yankin Benaadir, inda ya kammala karatunsa na jami'ar ƙasar Somaliya a shekarar 1975.
Shekarun aiki
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1977 ya shiga aikin soja a ƙasar Somaliya inda ya samu horo na farko a makarantar Janar Daud. Kamfanin dillancin labaran SONNA ya bayar da rahotan cewa, ya samu horon kwamandojin ƙasashen Amurka da Jamus, kuma ya taɓa zama mai horas da sojoji a wata makarantar horas da su. Bayan yaƙin basasar Somaliya, ya zama Daraktan Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa ta Somaliya.
Nasarori
[gyara sashe | gyara masomin]An naɗa Janar Abdi Hassan Mohamed a matsayin ƙaramin jakadan Somaliya a Djibouti a shekarar 1989. Daga shekarar 2007 zuwa 2008 ya kasance babban kwamandan sojojin ƙasar Somaliya, kuma daga shekarar 2008-2019 ya kasance mai kula da sojojin ƙasar Somaliya a ƙasar Saudiyya.
A watan Afrilun 2019, an naɗa shi mataimakin kwamandan sojojin ƙasar Somaliya, kuma a ranar 22 ga watan Agusta, 2019 aka naɗa Janar Abdi Hassan Mohamed a matsayin kwamandan 'yan sandan Somaliya.